Burkina Faso ta dakatar da lasisin wani sanannen gidan rediyo, Radio Omega, na tsawon wata uku bisa zargin cin mutuncin gwamnatin sojin kasar ta hanyar kiranta da “gwamnatin da ta karɓe mulki”.
Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasar (CSC) ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, inda ta ce gidan rediyon ba zai iya watsa shirye-shirye ko wallafa wani abu a kafafensa na sada zumunta ba har sai bayan wa’adin.
Hukumar ta ce wani labari da gidan rediyon ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 30 ga Yuli na ɗauke da kalmomi masu cin mutunci da kuma kin jinin gwamnati.
A cikin labarin da gidan rediyon ta ya wallafa, ya ce: “Cote d’Ivoire tana yawan fuskantar zargi daga gwamnatin sojin Burkina Faso kan bai wa ‘yan adawa mafaka da kuma hada makirci”, sannan ta kira gwamnatin Burkina Faso da “junta”, wato gwamnatin sojin ta ta ƙwace mulki.
CSC ta bayyana wannan kalma da “batanci da rashin da’a”.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka dakatar da Radio Omega ba, domin ko a watan Agustan 2023 sai da aka dakatar da shi na wata guda bayan ya yada hirar wani kakakin kungiyar da ke goyon bayan dawo da tsohon shugaban Nijar, Mohamed Bazoum, da aka hambarar.
Tun bayan hawan Ibrahim Traore kan mulki bayan juyin mulkin da ya yi a Satumban 2022, gwamnatinsa ta dakatar da kafafen watsa labarai da dama – daga ciki har da gidan rediyo da talabijin na Faransa waɗanda suka haɗa da LCI da RFI da France 24 – inda wasu ‘yan jarida na ƙasar kuma aka tilasta musu gudun hijira.
