Masu ruwa da tsaki a kasuwar Dawanau a Kano sun ce, farashin kayan abinchi da ake fitarwa kasashen ketare na ci gaba da sauka.
A hirar Premier Radio da sakataren Kungiyar ‘yan kasuwan, Kwamared Rabi’u Abubakar Tunfafi ya ce, sauyin yanayi da aka fara shiga ya taimaka wajen saukar Farashin wasu kayyayyakin abinci.
“Duk da kalubale da ake samu na wasu kamfanonin da suke rike kayan abinchi a wasu jihohin Najeriya, Farashin kayan abincin na cigaba da sauka”. In ji shi.
Daga bisani mahukunta Kasuwar ta Dawanau sun ce za su cigaba da kokari don saukaka farashinsu domin al’umma su amfana.
