
Bikin ya samo asali ne daga maguzancin Turawa da kuma addinin Nasara shekarun aru-aru da suka wuce
Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa bikin ranar masoya ta duniya da aka fi sani da Valentine’s Day haramun ne a addinin Musulunci.
A wani hoton bidiyo mai tsawo na shehun malamin da aka a shafukan sada zumunta na intanet a ranar Juma’a 14 ga watan Fabarairu a ranar da ake bikin, shehun malamin yayi dogon sharhi kan asalin bikin.
Malamin ya kuma ce, Musulunci na girmama soyayya ta gaskiya wadda ake gudanarwa bisa tsoron Allah kuma ya halasta masoya su yi wa juna kyauta, domin hakan yana kara dankon soyayya. Amma ba sai a wannan rana da aka kebance ba.
don haka bayar da kyautuka da niyyar bikin ranar 14 ga watan Fabrairu ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.