Shugabancin kasuwar kayan marmari da ke Kano ya sha alwashin rage farashin kayayyaki ne domin saukaka wa jama’a da kuma neman lada.
Shugaban kasuwar Malam Safiyanu Abdullahi CK, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da wakilinmu, Sani Kassim Auwal.
‘Yan kasuwarmu za su rage farashin kayayyakin ne da kimanin kashi 15 zuwa 20 cikin 100.” in ji shi.
Shugaban ya kuma ce, ‘yan kungiyar na daga cikin manyan kasuwannin da za su shiga Baje Kolin kayan masarufin Azumi, wanda gwamnatin Kano da ‘yan kasuwa suka shirya a dandalin baje koli dake titin Zoo a Kano.
Masu sayen daidai ko na dilla ko kuma na sari na iya ziyartar wurin domin samun rangwame.
Shugaban kasuwar ya kuma shawarci masu sayar da kayan marmari a cikin unguwanni da su saukaka farashi ga al’umma kamar yadda suka samu kayayyakin da sauki.
