
Kafar yada labarai ta BBC Hausa, taki karbar takardar ajiye aiki, da shugaban sashin Hausa na kafar, malam Aliyu Tanko ya danka mata a jiya Alhamis, inda ta dakatar da shi tsawon watanni uku domin yin bincike.
Wanann na zuwa ne bayan zarge-zargen cin zarafi da gallazawa da tsohuwar ma’aikaciyar tashar, Halima Umar Saleh ta yi a kwanakin baya.
Hirar da ta yi ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan Arewa24 ta goge bidiyon, abin da ya haifar da zargin tsoma baki daga wasu bangarorin.
Wata majiya ta ce an aike da ƙorafe-ƙorafe ma su yawa daga ciki da wajen gida zuwa hedikwatar BBC dake London, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Tuni dai babban ofishin BBC dake Landan ya turo tawagar bincike zuwa Abuja, karkashin mataimakin shugaban kafar Jonathan moro, domin yin bincike.
Jaridar solacebase ta ruwaito cewa anki karbar ajiye aikin nasa ne, saboda rashin bin ka’idoji, kuma a cewar mahukuntan ba zai iya ajiye aiki a lokacin da ake bincike kansa ba, yayin da aka dakatar da shi, kuma idan harma zai yi hakan to dole sai ya biya BBC albashin watanni biyu.