
Wasu da ba a san ko suwaye ba sun yiwa wani yaro mai suna Muhammad Gambo yankan rogo a garin Zango Biyu dake mazabar Zango a karamar hukumar Rimin Gado ta jihar Kano.
Yaron dan kimanin shekaru 5 an tsinci gawarsa ne da misalin karfe 10 na safiyar Lahadi, wanda hakan ya sa iyayensa da al’ummar garin cikin tashin hankali.
Wakilinmu, Ahmad Adamu Rimin Gado, ya tattauna da Laminu Ahmad Zango wani makwabcin gidan su Muhammad Gambo da aka kashe, inda ya shaida masa cewa sun samun gawar yaron kuma sun garzaya da ita zuwa ofishin yansanda na Rimin Gado domin gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata kisan.
Malam Laminu, ya tabbatar da cewa tuni aka gudanar da jana’izar yaron kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a yammacin Lahadi.