Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba shi da wata matsala ko rikici tsakaninsa da mataimakin sa, Kashim Shettima, sai dai sanbarka da kyakkyawar alaka.
Tinubu ya bayyana wannan a cikin wata sanarwar taya murna da ya fitar domin murnar cikar mataimakin nasa shekaru 59 na haihuwa.
A cikin sanarwar, shugaban kasa ya yi bayanin cewa Shettima mutum ne mai biyayya da kwazo da kuma jajircewa wajen bada hadin kai wajen gudanar da ayyukan gwamnati.
Tinubu ya kara da yabawa Shettima kan gudunmawar da ya bayar na taimaka masa wajen fahimtar halin da Najeriya ke ciki tun daga lokacin da aka rantsar da su a matsayin shugaban kasa da mataimakin sa a shekarar 2023.
