
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya karyata rahotannin da ke danganta shi da kawancen yan adawa, inda ya musanta cewa ya rungumi jam’iyyar ADC.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Boss Mustapha, ya ce bai taɓa shiga tattaunawa da kowa a jam’iyyun adawa ko abokan kawancensu ba.
Ya ƙara da cewa, ko da yake APC kamar kowacce jam’iyya tana da ƙalubale, mafita ita ce a gyara ta maimakon sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya.