Kwankwaso ba shi da jam’iyyar da ta fi PDP domin ita ta rene shi, inji Shugabanta na riko Ambasada Ilya Damagum.
Ya kuma bayyana hakan ne a hirarsa da BBC a ranar Talata.
Shugaban na mayar da martani ne kan kalaman da Kwankwason ya yi na cewa jam’iyyar PDP ta mutu, kuma ba za ta iya wata nasara ba a nan gaba.
“In ba ta mutu ba a wancan lokacin a 2015 a lokacin da suke ganin sun yi mata illa, to ban ga dalilin da za a ce ta mutu ba yanzu.
“Kuma kada Kwankwaso ya manta jam’iyyar PDP ita kadai ce ke iya cin zabe idan aka cire (jam’iyyar) masu mulki.
“Shi kansa Kwankwason da ya ce PDP ta mutu, ai bai yi wa kansa adalci ba, domin ai ya dauki jam’iyya amma jiha nawa ya ci. Inji shugaban
Damagum ya kuma ce, basu cire tsammani Kwankwaso zai zo a tafi da shi a PDP ba domin fuskantar azzalumar gwamnatin Tinubu a babban zabe mai zuwa.
Ya jaddada cewa a yanzu haka a shirye suke su karbi duk wasu ‘ya’yansu da suka yi fushi suka tafi wasu jam’iyyu, ciki har da Sanata Kwankwanson.
Shugaban jam’iyyar na riko ya kuma bugi kirji da cewa jam’iyyarsu ta PDP ita ce har yanzu bayan shekara 26 take amsa sunanta na PDP ba ta sauya ba, kuma take da gwamnoni da sanatoci zababbu a kowane sashe na Najeriya.
Ya ce yau a Najeriya idan aka cire PDP, aka hada jam’iyyu hudu ba za su iya cin zabe ba.
Kuma PDP jam’iyya ce da a kodayaushe take karbar duk wani danta da a duk lokacin da ya yi fushi ya tafi idan ya dawo tana karbarsa kuma ta ba shi dama kamar kowa.