
Aƙalla mutane biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon tashin wani bam da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka dasa a ƙaramar hukumar Gujba ta Jihar Yobe.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Satumba, da misalin ƙarfe 2:30 na rana, a kan hanyar Damaturu–Buni Yadi, kusa da ƙauyen Madiya.
Masani kan harkokin tsaro a Arewa maso Gabas, Zagazola Makama, ya bayyana cewa bam ɗin ya tashi ne a lokacin da ‘yan sa-kai ke gudanar da sintiri a yankin.
An tabbatar da mutuwar Kinnafi Modu dan shekara 35 da kuma Mamman Kasaisa dan shekara 27, yayin da wasu ‘yan sa-kai biyu suka samu munanan raunuka kuma aka garzaya da su Asibitin Gwamnati na Damaturu domin kulawa.
Jami’an ‘yansanda da na leƙen asiri sun isa wurin da abin ya faru, sun kuma taimaka wajen kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu tare da ɗaukar matakan tsaro.
An ƙara tsaurara matakan tsaro a kan hanyar Damaturu–Buni Yadi, domin dakile yiwuwar sake kai irin wannan hari.