
Babban jami’in diflomasiyyar Amurka Marco Rubio ya ce, Isra’ila ta yi gaban kanta ne ta kai wa Iran hari yana mai cewa ba hannun Amurka.
Rubio ya fadi hakan ne a matsayin martanin kasar ga hare-haren da Isra’ila ta kai Teheran babban biranin Iran a tsakar daren Alhamis.
Nan take ne Ministan Tsaron Isra’ila ya ce, sun kaddamar da hare-haren ta sama kan Iran, ta kuma ce ta kai hare-haren ne domin tarwatsa cibiyoyin nukiliyar Iran.
Isra’ila ta kira hare-haren na ba-zata da suna ‘Operation Zaki’, ta kuma kashe manyan jami’an sojin Iran da kuma fitattun masanan kimiya na kasar da suka hada har da Mohammad Bagheri da shugaban jami’an sojin Iran da Ali Shamkhani da Babban Mai Ba Jagoran Addini Na Kasar Shawara Ayatollah Ali Khamenei da kuma Babban Kwamandan Dakarun Juyin Juya Hali na kasar Janar Hossein Salami.
Shugaba Trump ya shaida wa kafar yada labarai ta ‘Fox News’ cewa, ya gargaɗi Isra’ila da ta kaucewa kai hari wanda ya kira zagon kasa ne ga tattaunawar da ake yi da Iran na taƙaita shirinta na nukiliya.
Bayan kai harin Isra’ila ta ayyana dokar taɓaci a kasarta don gudun hare-haren ramuwa da Iran za ta kai mata.