Babbar Kotu a Abuja ta fitar da ranar fara sauraron karar da aka shigar kan Wike
Tuni Kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 18 ga watan Fabrairu domin ci gaba da sauraron karar da wasu mabarata da marasa galihu suka shigar kan Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike inda suke kalubalantar kama su da tsare su.
Tun da farko, lauyan wadanda suka shigar da karar, Usman Chamo, ya shaida wa kotun cewa har yanzu ana ci gaba da cin zarafin wadanda yake karewa a babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce Wike na yaki da barace-barace a yankin.
