
Gidauniyar Kannywwood ta yi alhinin rashin tsohon jarumin finafinan Hausa.
A wata sanarwa da da Gidauniyara ta fitar wanda Daraktan Yada Labaranta Kabiru Mai Kaba Ya sa hannu, ta ce, rasuwar jarumin ya girgiza masana’antar da kuma masoya finafinan Hausa.
“Baba Karkuzu ya taka muhimmiyar rawa a ci gaban shirya finafinai da wasannin kwaikwayo na Hausa.
Tun a farkon shirye-shiryen talabijin a tashar Plateau State Television (PRTV Jos), inda ya shahara a shirin ‘Karakuzu na Bodara’ wanda ya ba shi sunan da ya yi fice da shi.
Daga nan, ya ci gaba da fitowa a finafinai da dama, inda ya tabbatar da matsayinsa a matsayin daya daga cikin gwarazan jaruman masana’antar.” In ji Sanarwar.
Gidauniyar ta kuma kwantanta marigayin a matsayin mutum mai cike da kwarewa da hazaka, wanda ya gina suna mai daraja a duniyar finafinai, ta kuma ce, rashinsa babban gibi ne da ba za a cike sauki ba.
Masana’antar Kannywood, abokan aikinsa, da duk masu kaunarsa sun yi matukar jimamin wannan rashi.
Kannywood Foundation na mika ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa, da ‘yan uwansa.
Muna rokon Allah Ya gafarta masa, Ya sa Aljannah Firdausi ta kasance makomarsa, kuma Ya ba iyalansa hakurin jure wannan rashi.