
Daga Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin kar-ta-kwana kan al’amuran tsaro a jihar Kano.
Kwamitin wanda zai kasance karkashin jagorancin Kwamishinan Kimiyya Da Fasaha Dakta. Yusuf Ibrahim Kofar Mata zai yi aiki da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Da yake jawabi yayin kaddamar da wakilan kwamitin a ofishinsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce, an zabo wakilan ne bisa cancanta tare da kyakkyawan fatan za su yi amfani da dabaru da gogewarsu wajen inganta zaman lafiya a jihar Kano baki daya.
Ya kuma ce, sun gano babban abin da yake haddasa rashin zaman lafiya shine zaman banza da yawo da matasa suke yi kan titi babu abin yi.
“Saboda haka ne ma tun zuwan gwamnatin nan muke bayar da horo daban-daban kan sana’o’in dogaro da kai. domin ba za mu zuba ido muna ganin ‘yan daba na kashe mutane ba, don haka dole ne mu dauki matakan kawo karshen matsalar”. Inji Gwamnan
A jawabin shugaban kwamitin, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya ce, za su yi iya kokarin su dan tabbatar da komai ya tafi daidai a jihar Kano.
“Za mu mayar da hankali kan zaman lafiya da dawo da tsaro kuma za mu yi kokarin wajen inganta zaman lafiya da sauya tunani da dabi’un matasa”. inji shi.
Wakilan kwamitin sun hada da Kwamishinan al’amuran Tsaron Cikin Gida Manjo-Janar Muhammad Inuwa Idris da Kwamishinan Yada Labarai Kwamared Ibrahim Abdullah Wayya da Babban Daraktan Ayyuka na musamman a gidan gwamnati AVM Ibrahim Umaru mai ritaya da shugaban vigilante na jihar Kano Alhaji Shehu Muhammad Rabiu da Muhammad Sanusi Balarabe da kuma Dakta. Danyaro Ali Yakasai.
Sauran sun hada da wakilci daga masarautu da malaman addini da rundunar soji da ‘yan sanda da ma’aikatar sharia da hukumar shige da fice da kuma hukumar kula da gidajen yari.
Wakilimmu na gidan gwamnati Aminu Abdullahi Ibrahim ya rawaito cewa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya horesu su gudanar da ayyukinsu bisa gaskiya da rikon amana.
