Ya ce babu ƙanshin gaskiya a zargin da ake yi masa na cewa yana shiga sharafin gwamnati har ya ce ga yadda za a yi.
Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, wannan neman haifar da baraka ne tsakaninsa da gwamna don biyan bukatar wasu tsirari.
Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata ya fadi hakan ne a hirarsa da BBC, ya kuma nuna rashin jin dadinsa da yadda wasu ke neman haifar wannan baraka don neman biyan wata bukata ta siyasa da kuma haifar da husuma.
“Wasu gani suke idan ya tsaya da ƙafarsa ya bar Kwankwasiyya, ba mamaki akwai masu neman gwamna a cikinsu” Inji shi.
Kuma su suke so idan gwamnan ya yi kuskure a mulki sai su hada da kungiyar kwakwasiyya da shi gwamnan gaba daya su soke su don cimma manufarsu.
Kwankwaso ya godewa gwamnan da dakatar da wadannan yan gaza-gani.
“Don haka ina so in godewa shi gwamna, dama da shi suke, to ya fito ya ce ahir” inji Kwankwaso.
A baya dai gwamna Abba Kabir ya barranta kansa da wadannan masu kiraye-kiraye na tsaya da kafarsa a inda ya jaddada mubayi’arsa da fa jagoran na su.
Kwankwaso ya karkare da cewa ya yi niyyar ya rika bayar da shawara ne a mulkin na gwamnatin Kano idan an nema, kuma abun da yake yi yanzu kenan.
.