Jami’an tsaro a Africa ta Kudu sun kama mutane sama da 1,000, bisa laifin haƙar ma’adanai ba bisa kaida ba, a wani samame da suka kwashe kwanaki da dama suna yi.
A wata sanarwa da rundunar ƴan sandan ƙasar ta fitar, ta ce, mafi yawan mutanen da aka kama ba ƴan asalin ƙasar bane, kuma basu da cikakkun takardun shaidar zama a ƙasar, duk da dai har yanzu ba’a bayyana ƙasashensu na asali ba.
Cikin watanni uku da suka gabata, ƙasar ta ƙara ƙaimi wajen tsaftace ayyukan haƙar ma’adanai, ganin yadda masu haƙa ba bisa ƙa’ida ba suka mamaye fannin.
A watan Janairun da ya gabata, mahukunta sun kama mutane sama da 2,000, inda a cikin adadi guda 1,128, ƴan asalin ƙasar Mozambique ne sai guda 473 da suka fito daga ƙasar Zambia, kana wasu 197 daga ƙasar Lesotho.
Bayanai sun ce yayin samamen, wasu guda 78 sun mutu bayan da suka buya a cikin ramukan haƙar ma’adanan, su kuma jami’an tsaro suka dakatar da shigar da abinci da ruwan sha.
Wannan mataki ya janyowa ƙasar suka daga wasu ƙasashen duniya da kuma ƙungiyoyin kare hakkin Ɗan Adam, suna masu zarginta da amfani da yunwa wajen kashe mutane.
