Aminu Abdullahi Ibrahim
Ƙungiyar tuntuɓa ta arewacin Najeriya, (ACF) ta musanta labarin kalubalantar hana ‘yan APC takara da shugaba Bola Ahmad Tinubu a 2027.
Yayin ganawa da manema labarai shugaban kungiyar a nan Kano Goni Farouk Umar, ya ce kalaman da kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito cewa kakakin yada labaran kungiyar Farfesa Muhd Tukur Baba na cewa bata goyon bayan shugaba Bola Ahmad Tinubu yayi takara shi kadai a APC a zaben 2027 ba da yawun kungiyar yayi ba.
Ya ce ko kadan abinda kakakin kungiyar ya fada ba da yawun su ya yi ba, kuma ko kadan basu ji dadi ba.
Ya ce su ba ‘yan siyasa bane kuma basa nuna bangaranci ga wadanda zasu tsaya zabe.
Ya ce suna alawadai ga kalaman nasa kuma a matakin jiha sun yi kira ga shugabancin kungiyar na kasa cewa nan gaba a tabbatar duk wanda zai yi magana akan siyasa sai an tantance.
Ya ce irin wannan ta taba faruwa a baya lokacin zabe yayin da wani wakilin kungiyar ya ce suna nuna goyon baya ga wani dan takara.
Sai dai ya ce ko a lokacin sai da suka barranta kansu da kalaman nasa bayan sun tabbatar ba da yawun kungiyar yayi ba.
Goni Farouk Umar, ya bukaci a jawa Farfesa Muhd Tukur Baba kunne tare da tabbatar da cewa haka ba ta sake faruwa ba.
Ya ce gabanin zaben 2023 (ACF) ta zauna da wakilan jam’iyu inda suka sanya hannu kan abubuwan da kungiyar ta nema.
Ya ce sun yi matukar farin ciki bisa yadda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kai kudiri majalisa don tabbatarwa da kananan hukumomi ikon cin gashin kansu.
Ya bukaci majalisa ta tabbatar da kudirin tare da kira ga hukumomin bincike su tabbatar ba a dauki kudaden al’umma anyi almubazzaranci da su ba.
