Gwamnatin ta ware Naira 180,000 a matsayin sadakin kowace amarya a karkashin shirin a jihar.
Gwanmatin za ta gudanar da daurin auren a ranar 27 Fabarairu na wannan shekarar 2025 a fadar Sarkin Gwandu da ke birnin Kebbi.
Shugaban kwamitin auren kuma mataimakin gwamman jihar, Suleiman Muhammad Argungu ne ya tabbatar da haka a ranar Lahadi.
Ya kuma ce, nasarar da aka samu a shekarar 2024 na aurar da ‘yan mata da zaurawan ne ya sa gwamnati ta sake bijiro da shirin a wannan lokaci.
Gwamnati ta bayyana cewa, ta na sane da yadda sadaki ke kawo cikas wajen daurin auren wasu daga cikin mazauna jihar, wanda ya sa gwamnati ta ware Naira 180,000 a matsayin sadakin kowace amarya a karkashin shirin.
An bayyana cewa an yi nasarar kashi 98 cikin dari na auren da aka daura a shekarar da ta gabata, inda bincike ya tabbatar da cewa ba a samu sakin aure da ya wuce biyu ba.
