
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da sabon harin da Boko Haram suka kai a Jihar Borno, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama ciki har da sojoji.
A cikin wani saƙon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Atiku ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai wajen yaƙi da matsalar tsaro.
Atiku ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da jama’ar Jihar Borno, da kuma Gwamna Babagana Umara Zulum.
Sannan ya yabawa gwamnan bisa ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar da abin ya shafa.
Atiku ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa waɗanda suka rasu, Ya kuma sanya su a Aljanna Firdausi.
Hakazalika, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen samar da zaman lafiya da tsaro.