Ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, ta sanar da shirin fara gudanar da zanga-zanga a jami’o’in gwamnati dake faɗin ƙasar nan, tare da barazanar tsunduma yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ta gaza biya musu buƙatunsu.
ASUU ta sanar da shirin nata ne a wata takarda da shugabanta Christopher Piwuna ya fitar bayan kammala taron su a Sokoto.
Ƙungiyar ta sanya ranar 28 ga watan Agusta a matsayin wa’adin da ta baiwa gwamnatin tarayya domin ta yi duba kan buƙatunta, ko ta ɗauki mataki na gaba.
Cikin buƙatun da ASUU ta ke neman gwamnatin ƙasar nan ta biya, har da na biya mata buƙatunta dake ƙunshe cikin daftarin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da ƙungiyar a shekarar 2009, tare da sabunta ta.
Ƙungiyar ta ce ta bi hanyoyi da dama don ganin an cimma matsaya tsakaninta da gwamnati, ciki har da rubuta wasiƙu, baya ga jan hankalin gwamnati kan lamarin, amma har kawo yanzu ta gaza wajen magance su.
