
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta ba wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu ta biya buƙatunta ko kuma ta shiga yajin aiki.
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa bayan taron majalisar zartarwar ƙungiyar da aka gudanar a jami’ar Abuja a ranar Lahadi.
“ASUU ta gaji da yadda gwamnati ke ci gaba da nuna halin ko in kula ga harkar ilimi, duk da tattaunawa da suka daɗe suna yi kan buƙatun ƙungiyar.
“Idan gwamnati ta ƙi amsa koken kungiyar cikin wa’adin kwanaki 14 da ta bayar, za ta fara yajin aikin gargaɗi na makonni biyu, wanda daga bisani zai iya rikidewa zuwa na sai-baba-ta-gani”. In ji sanarwar.
ASUU ta ce cikin buƙatunta akwai da bitar yarjejeniyar shekarar 2009 da samar da isassun kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i da biyan bashin albashin malamai da kuma samar da tsayayyen tsarin samun kuɗaɗen gudanarwar jami’o’in.