Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) tare da Gwamnatin Tarayya sun kammala tattaunawa kan sabunta yarjejeniyar shekarar 2009, wadda za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2026.
Sabuwar yarjejeniyar za a sake duba ta duk bayan shekaru uku domin tabbatar da ingantacciyar aiwatarwa.
Yarjejeniyar ta ƙunshi muhimman sauye-sauye da suka shafi inganta rayuwar malaman jami’o’i da kuma ƙara wa jami’o’in gwamnati kuɗaɗen tallafi.
Ma’aikatan jami’o’i za su samu ƙarin albashi da kashi 40 cikin 100.
Farfesoshi za su yi ritaya a shekara 70 tare da samun fansho daidai da albashinsu na shekara.
Jami’o’in gwamnati za su samu ƙarin kuɗi don gudanar da bincike, ɗakunan karatu, ɗakunan gwaje-gwaje, kayan aiki, da horar da ma’aikata.
Yarjejeniyar ta ƙara samar da ’yancin gudanar da jami’o’i da ’yancin ilimi, ta bai wa Farfesoshi damar zaɓar shugabanni kamar deans da provosts.
Ta kuma tabbatar da cewa ba za a hukunta malamai da suka yi yajin aiki a baya ba.
ASUU ta yi kira ga gwamnati da ta aiwatar da yarjejeniyar cikin gaggawa, tare da faɗaɗa tattaunawa da sauran ƙungiyoyin jami’o’i domin tabbatar da tsarin ilimi mai ɗorewa.
