Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano ya hana motoci masu bakin gilas shiga harabar asibitin.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Gudanarwa na asibitin, Usman Rabiu Mudi ya fitar a karshen mako.
Daraktan ya ce, an sa dokar hana motocin masu bakin gilashi shiga asibitin ne saboda yawaitar ayyukan laifi a asibitin.
Sanarwar ta kara da cewa, ma’aikatan asibitin da ke amfani da mota za su yi rajistar motocinsu a ofishin tsaro don samun tambarin tantancewa da izinin shiga.
Aminiya ta rawaito cewa, Shugaban Tsaro na asibitin, Sani Ahmad Mahmud na cewa, matakin hana shigar motoci masu bakin gilashin na cikin manufofin kare ma’aikata da marasa lafiya da baki da ke zuwa asibitin.
“Wannan mataki ya zama wajibi saboda kalubalen tsaro da muke fuskanta. Ina kira ga jama’a su bi wannan doka tare da girmama ta, domin matakin yana cikin muradinsu,” in ji shi.
Wasu daga cikin jama’a sun yaba da matakin, suna ganin hakan zai rage yawaitar shigar miyagun mutane cikin asibitin inda suke amfani da wannan damar wajen aikata laifuka da ayyukan da ba su dace ba a harabar asibitin.
A cewar wani rahotanni, satar motoci da babura da sauran kayayyaki masu daraja ta yi yawa a cikin harabar asibitin mai girman gaske.
La’akari da cewa, wasu mutane na amfani da harabar asibitin wajen aikata ayyukan ashsha, wanda hakan ya sa mahukuntan suka dauki wannan mataki na hana motoci masu bakin gilashin shiga.
Ciki har da yunkurin sace mutane ta amfani da irin wadannan motocin da kuma aikata ayyukan laifi daban-daban da suka kunshi sata da aikata abubuwan da ba su dace ba a cikin harabar asibitin.
Sai dai motocin da ke ɗauke da marasa lafiya ko ma’aikata za su iya shiga, amma sai an bi ka’idojin tsaro na musamman.