
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sanar da samun fam 616.6m, sai dai ta yi asarar kimannin Naira 33 471 585 000.00 watau Fam 17.7m a zangon kasuwanci daga 31 ga watan Mayun 2024.
Arsenal ta samu tagomashin karin kudin na £71.1m wajen nuna wasanta a talabijin da karin kuɗin shiga filin wasa £29.1m bayan kai wa zagayen na biyu da na karshe a kakar 2023/2024.
Mikel Arteta da ke jan ragama tana ta biyu a teburin Premier League, yayin da ƙungiyar mata ta Arsenal take ta ukun teburi a Women Super League da lashe League Cup.
Karin ƙudin shiga da ta samu kaso 32.1 cikin 100 ne daga £466.7m da ta sanar a Mayun 2023.
Yayin da asarar £17.7m kafin a kwashe haraji kaso 66 cikin 100 ne, kasa da hasarar £52.1m a gabaki ɗayan 2022-23.
Bayan da Gunners ta koma buga gasar zakarun Turai ta samu karin £262.3m daga £191.2m wajen nuna wasanta a talabijin da kuma £102.6m daga £131.7m a kallon wasanni a filin wasa.
A yanzu haka Arsenal ta samu riba wajen sayar da ƴan wasa da bayar da wasu aro da ya kai £52.4m daga £12.2m, an samu karin cajin kasuwanci £6.2m daga £18.4m.