Laftanar Ahmed Yerima matashin sojan da ya taka wa ministan Abuja birki tsallake rijiya da baya.
Rahotannin sun cewa wasu bata bata gari sun yi kokarin hallaka matashin sojan a yammacin Lahadin nan.
“Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 da rabi na yammacin ranar bayan da wasu mutane sanye da baƙaƙen kaya a cikin motocin Hilux guda biyu suka biyo motarsa da kokarin cim masa
“Cikin lura da ankarewa da manufarsu matashin ya tsere musu” in ji wata makiya ta rundunar sojan.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Yerima ya taka ministan Abuja Nyesom Wike birki a kokarinsa na rusa wani gini da ya ce an yi ba bisa ka’ida ba.
Jarumtar da matashin sojan ya nuna da kafewarsa na umarnin da aka ba shi na Kula da wurin ta sa ya yi farin jini da ɗaukaka a idon jama’a.
