
Jamiyyar hamayya ta ADC zargi hana mambobinta yin taruka a wasu jihohin kasar, lamarin da jagororinta suka ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
Shugabannin jam’iyyar na kasa sun bayyana hakan ne a wani taro da suka yi a Kaduna, ranar Alhamis.
Sun bukaci da a gaggauta gudanar da bincike da kuma hukunta duk wadanda aka samu da hannu a hare-haren da aka kai wa wasu ‘ya’yan jam’iyyar a jihohin Kaduna da Kebbi da kuma jihar Katsina domin hana su taro.
Ayarin shugabannin jam’iyyar ta ce ta ziyarci jihar ta Kaduna domin jajantawa reshenta jihar a kan harin da wasu gungun bata gari suka kai wa ‘yan jam’iyyar da makamai a lokacin da suke wani taro a makon jiya, lamarin da ya jikkata wasu ‘ya’yan jam’iyyar. “Kuma hakan ba zai ba zai karya mana gwiwa ba”. in ji ayarin shugabannin a Kaduna.
‘Yan ayarin shugabannin sun kuma yi zargin cewa sun gamu da cikas a yunkurinsa na ganawa da mambobin na jihar Kadunan a sakatariyar jam’iyyar da ke jihar.