Rikicin da ake gwabzawa a kan iyakar Thailand da Cambodia ya shiga kwana na uku a yau Asabar, yayin da ɓangarorin biyu ke iƙirarin sun ɗauki matakin ne domin kare kansu a rikicin da suke, tare da yin kira a hau teburin tattaunawa.
Sama da mutane 30 ne suka rasa rayukansu tare da raba wasu sama da dubu 130 da muhallansu, a faɗan mafi muni da ake yi tsakanin makwaftan junan da ke kudu maso gabashin nahiyar Asiya cikin shekaru 13 da suka gabata.
Ɓangarorin biyu dai sun tabbatar da gwabza rikicin da suka yi da sanyin safiyar yau Asabar, a lardin Trat da ke gabar tekun ƙasar Thailand da kuma lardin Pursat na Cambodia.
Ƙasashen biyu dai sun fara musayar yawune tun bayan kashe wani sojan Cambodia a ƙarshen watan Mayu a wani takaitatcen gumurzun da suka yi, lamarin da yasa kowa ne ɓangare ƙara ƙarfafa dakarunsa da ke kan iyaka.
Ya zuwa yau Asabar, Thailand ta ce an kashe sojojinta 7 da fararen hula 13 a rikicin, ya yin da kakakin ma’aikatar tsaron Cambodia, Maly Socheata ta ce an kashe musu sojoji 5 da fararen hula 8.
