Ya ce, ana yi mi shi barazanar ce don kawai ya ce shugaban ya bi titunan kasar nan, ya kuma je asibitoci ya gane wa idonsa halin da ‘yan kasa ke ciki.
Dantakarar shugaban kasa a Jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya ce an fara barazana ga rayuwarsa saboda kalamansa a kan shugaba Tinubu.
A sakonsa na sabuwar shekara, Peter Obi ya caccaki salon mulkin gwamnatin tarayya, inda ya ba da jerin shawarwari ga shugaban kasa.
Peter Obi ya bukaci shugaban ya rika bin titunan kasar nan, sannan ya rika ziyartar asibitocin Najeriya don gane wa idonsa halin suke ciki.
Sai dai duk nuna damuwarsa kan lamarin bai fadi matakin da ya yi shirin dauka ba.
alama fadin hakan ya fusata wasu, domin wani r Felix Morka ya zarge ni da wuce gona da iri, kuma zai dandana kudarsa, a cewarsa.
“Ni ba na tunanin na karya doka a kalamaina kan shugaban kasar da har za a fara yin barazana ga rayuwata” in ji shi.
Peter Obi bai fadi matakin da zai dauka ba kan wannan ba.