Mojisola Lasbat Meranda ta kafa tarihin zama mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar majalisar dokokin jihar Legas.
Hakan ya biyo bayan tsige Mudashiru Obasa wanda ke kan kujerar tun a shekarar 2015, biyo bayan zarge-zargen da ake masa, wanda suka hada da rashin da’a, da cin hanci da rashawa.
A shekarar 2015 aka zabi Mojisola Lasbat Meranda a matsayin yar majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar Apapa 1 karon farko, yayin da aka sake zabenta a shekarar 2019 da 2023.