An saki sauran ɗaliban makarantar sakandiren St. Mary’s Catholic dake Papiri a Jihar Neja da yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Wanda kuma hakan ke nuni da cewa, wadanda aka ceto baki dayan su daga kan daliban zuwa malaman sun kai guda 230.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin mai bawa sugaban kasa shawara kan harkokin tsaron Ƙasa Malam Nuhu Ribadu ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi.
Wannan ci gaban da aka samu, ya kawo ƙarshen tashin hankali da iyalan waɗanda abin ya shafa suka shiga, da kuma nuni da gagarumar nasara da hukumomin tsaron suka samu wajan ceton daliban.
An sace ɗaliban makarantar sakandirin ne lokacin da ’yan bindiga suka kai hari makarantar kwanan, wanda kuma hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce a fadin kasar nan.
Hukumomi sun bayyana cewa sakin dukkanin daliban ya biyo bayan matsin lambar jami’an tsaro suke yi babu kakkautawa da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomi tsaro.
