
Rantsar da sabon shugaban APC a taron jiga-jigan Jam'iyyar a Abuja
Kwamitin Zartaswa na Jam’iyyar APC ya zabi Ministan Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa
An kuma rantsar da shi nan take a wajen taron da aka gudanar a ranar Alhamis.
Nentawe ya sha rantsuwar ne da misalin ƙarfe 02:50 na rana a gaban manyan jiga-jigan jam’iyyar yayin taron NEC karo na 14 da ya gudana a ɗakin taro na fadar gwamnatin tarray a Abuja.
Sabon shugaban ya fito daga Jihar Filato shiyyar Arewa ta Tsakiya, kuma shi ne ɗan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a zaɓen 2023.