
Rikici ya barke a Karama Hukumar Rano wanda hakan ya jawo hasarar rayuka da kone ofishin ‘yansanda da kuma sassara DPO.
Wani mazaunin garin ya shaidawa Premier radio cewa ana zargin Baturen ‘yan sandan garin Baba Ali, da yiwa wani matashi dukan kawo wuka, wanda daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.
Wanda hakan ya fusata mutanen gari, suka kuma bazama ofishin ‘yansandan domin bayyana fushinsu.
A kokarinsu na kare kai ‘Yansandan suka dau matakin kare kai tare yin harbi a inda ake zargin sun jikkata ta mutane da dama.
Musamman yayin da fusattun matasan da jama’a suka soma yi musu ruwan duwatsu.
Shaidar gani da ido ya shaidawa Premier Radio cewa lamarin yayi kamarin da aka kai ga jiwa baturen yan sandan mummunan rauni da kuma kone ofishin ‘Yan sanda na yankin.
Mun tuntubi jami’an gwamnati a Karamar Hukumar, sun tabbatar da cewa an samu rikici, amma za su bayar da cikakken bayani anjima kadan.