An kashe ‘yan Sudan 16 a tarzomar da ta barke a yankin Al Jazirah na kasar Sudan
A ranakun Alhamis da Juma’a ne rikicin ya barke a Juba babban birnin Sudan ta Kudu da kuma wasu wurare na kasar.
Wasu masu zanga-zanga ne suka fusata kan abin da suka yi imani cewa da hannun sojojin Sudan da kuma kungiyoyin kawayenta wajen kashe-kashe a Al Jazirah.
Rundunar sojin Sudan ta yi tir da abin da ta kira ‘’cin zarafi na daidaikun mutane’’ a birnin Al Jazira.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun dora alhakin hare-haren na kabilanci a kan fararen hula da ake zargi da tallafa wa ‘yan tawayen rundunar RSF.
A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Sudan ta Kudu ta fitar, ta ce, ‘’an kashe ‘yan Sudan 16 a jihohi hudu.’’
‘Yan sanda za su ci gaba da sintiri a kasuwanni da wuraren zaman jama’a domin al’ummar Sudan, a cewar wata sanarwar.
A ranar Juma’a ne, gwamnati ta kafa dokar hana fitar dare zuwa safiya, wacce har yanzu take aiki.
Akalla mutane 24 ne aka kama kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike, in ji rundunar sojin Sudan ta Kudu a wata sanarwa ta daban da ta fitar.