Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan wasu manoman da suke aikin girbin amfanin gona a yankin Mbor na masarautar Mushere na Ƙaramar hukumar Bokkos a Jihar Filato.
Rahotanni su ce an kashe mutane uku tare da jikkata wasu biyu a yamacin Laraba.
A hirarsa da Daily Trust, Shugaban Ƙungiyar matasan Mushere, Kopmut Monday ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
“ ’Yan bindigar sun kai farmaki wurin ne inda suka buɗe wuta kan manoman da ke cikin aikin girbin amfanin gona, inda ya ce manoman sun tsere domin tsira da rayukansu. In ji shi.
Shugaban ya kuma zargi Fulani makiyaya da kai wa mambobinsu hari, domin waɗanda ake zargin “mazauna garin Rongjing in ji shi.
Monday ya kuma ce, al’ummar yankin sun sha fama da irin wannan hari ida ko a ranar 26 ga watan Mayu an kashe mutane bakwai.
Ya kuma kara da cewa, al’ummar da aka kai wa harin na baya-bayan nan, sun yi kira ga jami’an tsaro da su tura isassun ma’aikata don dawo da zaman lafiya a yankin saboda mazauna yankin ba za su iya gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba cikin kwanciyar hankali.
