Jami’an tsaron kasar Habasha sun kama mutum 12 da ake zargi da shirin kai hari kan shugabannin kasashen Afrika, yayin da suke gudanar da taron AU a birnin Addis Ababa.
Rahotanni sun ce an gurfanar da su gaban kotu, inda sunayen mutum 15 suka bayyana, ciki har da wani jami’in ‘yan adawa da ake zargi da alaƙa da ƙungiyar Fano.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na daga cikin mahalarta taron, tare da sauran shugabannin kasashen Afrika.
Jami’an tsaron Habasha sun ce suna ci gaba da bincike kan lamarin, domin gano ko akwai wasu da ke da hannu a shirin.
