
Hukumomin tsaro a Chadi sun kama dan Muhammad Yusuf mai suna Abdarhman Yusuf, wanda ake zargin yana da alaƙa da ayyukan mayakan Boko Haram
Rahoton mai bibiyar harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya tabbatar da cewa an kama shi ne tare da wasu mutane guda biyar da ya ke jagoranta.
Wasu rahotanni sun ce Abdarhman Yusuf ɗan uwa ne ga shugaban kungiyar ISWAP, Habib Yusuf, wanda aka fi sani da Abu Mus’ab Abarnawi.
Biyo bayan kama Abdarhman, hukumomi sun tunasar da lokacin da aka kama Muhammad Yusuf, wanda ya kirkiro kungiyar Boko Haram a Najeriya a shekarar 2009.
Daga bisani, an hallaka Muhammad Yusuf a Maiduguri, jihar Borno, yayin da aka ci gaba da yaki da ta’addanci a yankin.