
Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya ƙaddamar da babban taron ƙasa na Nijar wanda zai tsara dokoki kan yadda za a tafiyar da ƙasar a karkashin mulkin soji na riƙon ƙwarya.
Ana gudanar da taron ne a babban ɗakin taro na ƙasa da ƙasa da ke Yamai inda ake sa ran shafe kwanaki huɗu ana gudanar da taron.
Taron ya samu halartar tsofaffin shugabannin Nijar da tsofaffin shugabannin majalisar dokokin ƙasar da tsofaffin firaministoci na ƙasar da mambobin gwamnatin soji ta riƙon ƙwarya ta Nijar da wasu baƙi daga Burkina Faso da Mali da wasu ƙasashen.
Mutum 716 za su halarci wannan taron wanda ake sa ran zai dasa shika-shikan mulkin dimokuraɗiyya a Nijar kuma ana kyautata zaton taron zai bayar da shawara kan tsawon wa’adin gwamnatin riƙon ƙwarya.
A lokacin da yake jawabin buɗe taron, Janar Tiani ya ce an sanar da gudanar da wannan taron tun bayan da suka karɓi mulki amma sai yanzu ake gudanar da shi saboda yadda Nijar ɗin ke fuskantar barazana daga wasu ƙasashen duniya don ta buƙaci cin gashin kanta.
Shugaban na Nijar ya kuma ce sakamakon har yanzu ƙasar na ci gaba da fuskanatar barazana, ya buƙaci haɗin kan ‘yan ƙasar domin a gudu tare a tsira tare.