Ya gamu da ajalinsa ne a wani harba-harbe da ya rutsa da shi a birnin Stockholm.
Mutumin mai suna Salwan Momika dan kasar Iraƙ ne mazaunin Sweden da ya sha lalata Alƙur’ani a kasar a shekarun baya.
Takadarin ya gamu da ajalinsa ne a ranar Alhamis kamar yadda wata kotu a Stockholm ta tabbatar.
Kafar watsa labaran Sweden ta ruwaito cewa Salwan ya mutu ne sakamakon harbe-harben bindiga da ya rutsa da shi daya daga biranen ƙasar.
Salwan Momika mai shekara 38, ya sha ƙona Alƙur’ani da kuma lalata shi a Sweden.
Bidiyoyinsa a lokacin da yake lalata Alƙur’ani sun bazu a shafukan Intanet.
Lamarin da ya janwo mutane da dama musamman a ƙasashen Musulmi suka harzuƙa, tare da yin zanga-zanga kan hakan.
Kafin rasuwarsa, kotun Sweden na gudanar da bincike a kansa a bisa zargin tayar da hankulan ƙabilu a kasar.
Wata kotu a birnin Stockholm ta bayyana cewa an ɗaga sanar da wani hukuncin da aka yi niyyar yi a kansa a ranar Alhamis a wata shari’a kan haddasa husuma a tsakanin kabilun kasar
Alƙalin kotun da ke shari’ar Goran Lundahl ya tabbatar da cewa da ya mutu Momika ne, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Sweden TT ya ruwaito.