Masu ikirarin jihadi sun hallaka akalla manoma 40 a jihar Borno, a cikin jerin tashe-tashen hankulan da suka afkawa yankin a baya-bayan nan.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Usman Tar, ya fitar ya bayyana cewa mayakan ISWAP sun kai hari a garin Dumba inda suka yi wa dimbin manoman kofar rago da harbe su har lahira.
Rahotannin farko sun bayyana cewa an hallaka manoma 40, yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka ɓace domin hadasu da iyalansu.
Gwamnatin jihar ta umarci dakarun da ke yaki da masu ikirarin jihadi su bi sawu tare da kawo karshen masu tada kayar bayan da ke gudanar da harkokinsu a garin Dumba da sauran maboyansu a yankin tafkin Chadi.