
An ga jinjirin watan Shawwal a Najeriya da ya kawo karshen watan azumin Ramadan a Najeriya.
Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ne ya sanar da ganin watan a wani jawabi da yayi ga fadarsa a ranar asabar da dare.
Sarkin Musulmi ya ce, an samu labarin ganin watan ne a garuruwan Maiduguri da Daura da kuma Zazzau.wanda ya hakan ya kawo karshen azumin watan ramadana na wannan shekara ya kuma tabbatar da cewa gobe Lahadi Sallah.
Tun kafin sanarwa ganin watan a Najeriya mahukuntan kasar Saudiyya suka sanar da gani watan a kasar.
Kasar Nijar ita ma ta bayar da sanarwar ganin watan a manyan garuruwan kasar.
da farko daya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Najeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da labarain ganin watan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Kafin Sarkin Musulmi ya bayar da sanarwar a hukumance.