An fara samun kwanciyar hankali jim kaɗan bayan tsagaita wuta tsakanin India da Pakistan, bayan shafe kwanaki huɗu suna faɗa da juna.
Sai dai wakilin BBC ya ce bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wutar, anji ƙarar ababen fashewa na mintuna a yankin Kashmir.
Babban jami’in diflomasiyyar India Vikram Misri, ya shaida wa manema labarai cewa Pakistan ta karya yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma, yayin da ita ma Pakistan ɗin ta zargi Indiya da aikata makamancin haka.
Sai dai ana ganin rikici tsakanin kasashen biyu y afara daukar wani sabon Salo inda Sojojin Pakistan suka ce sun soma kai hare-haren ramuwar gayya akan Indiya, bayan sun zargi Delhi da kaddamar da munanan hare-haren makamai masu linzami a sansanonin sojojinta na sama guda uku.
India ba ta yi martani ba a kan wannan batu. Sai dai kasashen biyu na cigaba da zargin juna da ta’azzara rikici tun bayan hari da aka kai kan masu yawon-bude a yankin Kashmir a cikin watan da ya gabata.
Pakistan ta mayar da martani mai zafi tana mai jadadda cewa, a shirye take ta ce cas ga duk wanda ya fadamata kulle.
Wadannan su ne kalaman da sojojinta ke ambata bayan kaddamar da farmakin da suka bayyana da Operation Bunyanun Marsoos.
