‘Yan sandan jihar Kano ta sanar da nasarar cafke jagororin fadan daba a tsakanin Kofar ‘yan Kofar Mata da Zango a birnin Kano.
Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanar da hakan a yayin gabatar wa da manema labarai matasan da ake zargi a hedkwatar ‘yan sandan a ranar Alhamis.
matasan Kabiru Jamilu, da aka fi sani da AWU dan shekara 21 da kuma Umar Garba dan shekaru 32, dukanninsu mazauna unguwar Zango ne
“Binciken ‘yan sanda na farko-farko ya tabbatar da cewa, Kabiru, ne ya kitsa rikicin dabar tsakanin matasan Kofar mata da kuma na Zango, shine kuma ya jagoranci fadan dabar” inji shi.
Kakakin ya kuma ce, dakarun yan sandan da aka girke a mahadar Kofar Mata kusa da unguwar zango da kuma asibitin kwararru na Murtala Muhammed ne, suka kama matasan a ranar 24 ga watan Disamba 2024, da misalin karfe 8:40pm na dare.
A cewarsa, za a mika matasan babban sashin gudanar da binciken manyan laifuka rundunar kuma da zarar an kammala za a gurfanar da da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.
Sannan ya ce,”Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Salman Dogo Garba, ya bukaci mazauna Kofar Mata da Zango da su kasance masu ba wa ‘yan sanda hadin kai, musamman wajen bayar da bayanan sirri don magance matsalar baki daya”.