Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa sojojin kasar sa sun kai wani mummunan hari kan wasu cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, ciki har da muhimmin cibiyar sarrafa uranium ta karkashin kasa a Fordo.
Sanarwar hakan da Shugaban ya wallafa a shafin sa na X na zuwa a matsayin wani mataki da Amurkan ta dauka mai cike da bada mamaki, la’akari da kwanaki biyu kenan kacal da Shugaba Trump ya bayyana cewar zai yanke shawara cikin makwanni biyu domin ganin ko Amurka za ta shigarwa kawarta Isara’ila kaiwa Iran din hari.
Tun da farko a jiya Asabar an sami rahotannin cewa wasu jiragen yakin Amurka wadanda ke dauke da bama-baman da ake kira bunker buster sun nufi Iran, inda Shugaba ya bayyana cewar dole ne Iran din ta dakatar da shirin ta mallakar makamin nukiliya.
Rahotanni dai sun bayyana cewar tun ajiyan Asabar, Iran ta yi barazanar daukar fansa kan sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya idan Trump ya kai mata hari.
kamfanin dillancin labarai na Anadolu sun ce kasar Iran ta riga ta kwashe kayayyaki da kayan aikin ta daga cibiyoyin uku kafin harin na Amurka ya afku.
