Ma’aikatar harkokin wajan Amurka ta tabattar da soke bisa ta shiga kasar ga shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da wasu jami’ai Faalasdinawa 80.
Wannan mataki dai zai hana Mahamoud Abbas na zuwa ne bayan hallatar taron koli na MDD da za a yi a watan Gobe a birnin Washington na kasar Amurka.
A taron da za’a gudanar dai aka yi tunanin kasashe da dama sun kudurci anniyar amincewa da yancin kafa kasar Falasdinu a matsayin kasa mai ƴancin gashin kai, wanda shi ne babban burin mutanen yankin.
Isra’ila ta dage kai da fata cewa bai kamata a ba Falasɗinu ƴanci zama cikakkiyar ƙasa ba, kuma tana samun goyon bayan Amurka.
