Ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya gargadi Amurkawa mazauna Najeriya kan yiwuwar gudanar da zanga-zanga mai tsanani a Abuja a Larabar nan.
Cikin wata sanarwa da ofishin ya fita ranar Laraba ta ce ta samu rahoton za ayi zanga-zangar ne mai alaka da hare-haren Amurka akan Iran.
Ta ce irin wannnan zanga-zanga a baya ta rikide zuwa tarzoma.
Ta kuma nemi Amurkawa su sake duba tsare-tsarensu na tsaro tare da barin wayoyinsu da caji da daukar katin shaida da kuma sanya ido a guraren da suke zuwa da suka hada da shaguna da sinima da guraren ibada.
Gargadin na zuwa ne yayin da aka shiga kwanaki hudu da Amurka da Isara’ila suka kaddamar da yaki akan kasar Iran lamarin da ya kai ga kashe jagoran addinin kasar Ayatollah Ali Khamenei.
Itama Iran takai manyan hare-hare Isra’ila da sansanonin sojin Amurka dake gabas ta tsakiya
