Hamas da Isra’ila na ci gaba da samun saɓani game da sabon ƙudurin da Amurka ke mara wa baya na tsagaita buɗe wuta a Gaza.
Wakilin na musamman na Amurka a gabas ta tsakiya Steve Witkoff, ya ce matakin da ƙungiyar ta Hamas ta ɗauka na yin gyara ga kundin ba abu ne da za a amince da shi ba.
Ita dai Hamas ta ce za ta saki fursunonin yaƙi huɗu a ranar farko, biyu a rana ta 30, sai kuma huɗu a ranar ƙarshe ta yarjejeniyar, wato rana ta 60.
Ta kuma buƙaci ba da damar shigar da kayan jin-ƙai nan take, tare da yin tayin ajiye shugabancin yankin a siyasance, don ba da damar kafa gwamnatin ƴan takarda, da za ta jagoranci yankin.
Buƙatar ƙungiyar ta neman tattaunawar da za ta kai ga kawo ƙarshen yaƙin da kuma janye sojojin Isra’ila baki ɗaya, sun kasance wani batu da ke ci gaba da kawo cikas.
