Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa zai saka Najeriya cikin jerin ƙasashe da ake da damuwa a kansu, saboda zargin yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla.
Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na dandalin sada zumunta na Truth Social a yammacin ranar Juma’a.
“Shi ne mataki mafi ƙanƙanta da ya dauka zuwa yanzu.
“Kiristanci na fuskantar babbar barazana a Najeriya. “Ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke aikata wannan kisan gillar.
Saboda haka na ayyana Najeriya ƙasar da ake da damuwa a kanta”. In ji shi.
- Chaina da Amurka na shirin dinke barakar tsakaninsu
- Amurka ta haramtawa fitaccen dan Najeriya shiga kasarta
Trump ya kuma ce, ya bai wa ‘yanmajalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole umarnin fara bincike kan hakan kuma su kai masa rahoton sakamakonsa.
A farkon watan nan ne wani sanata a Amurkan ya yi zargin yi wa Kiristoci kisan gilla, wanda gwamnatin Najeriya ta musanta.
Masu lura da al’amura na cewa, zargin kisan gillar ya kunno kai ne tun lokacin da Kashim Shettima ya bayyana matsayin Najeriya na goyon bayan Falasdinawa a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a Amurka.
