Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bada umarnin rufe gidan Badeggi FM bisa zarginsu da taka rawa wajen haifar da rashin tsaro a jihar.
A cewar gwamnan ɗaukar wannan mataki ya zama wajibi domin tabbatar da zaman lafiya a ciki da wajen jihar.
Sai dai tuni kungiyar kare hakkin dan adam (Amnesty International) ta yi Allah-wadai da umarnin Gwamnan Neja
Amnesty ta ce zargin da gwamnan ya yi wa rediyon da cewa tana “haddasa tashin hankali” da kuma umarninsa na “a soke lasisinta” ya nuna karara yadda gwamnan ke amfani da iko da rashin yarda da ra’ayoyin masu suka.
Ta ce umarni na rufe tashar ba daidai ba ne kuma ba shi da wata hujja ta doka ko adalci.
Ta kara da cewa a daidai lokacin da ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya ke addabar jihar Neja ta hanyar kashe-kashe da korar al’umma daga gidajensu, maimakon kare rayuka, sai gwamnatin jihar ta bige da zargin tashar rediyo wanda hakan nuna gazawar shugabanci ne.
Amnesty ta ce wannan wani yunkuri ne na dasa tsoro a zukatan ‘yan jarida da kafafen yada labarai a Najeriya, domin hana su gudanar da aikinsu cikin ‘yanci.
Ta ce ya kamata Gwamna Bago ya janye umarnin na nasa nan take.
Ta ce la’akari da dokokin Najeriya, gwamnan ba shi da ikon rufe tashar rediyo.
