Aminu Abdullahi Ibrahim
Mamallaka filaye a unguwar Dangoro kusa da rigar fulani dake karamar hukumar Kumbotso sun gabatar da sallar Alkunuti kan zargin gwamnatin Kano da kwace musu filaye.
Sun gabatar da sallar ne ranar Asabar bisa ikirarin cewa gwamnatin Jihar Kano na yinkurin kwace musu filaye domin gina sabuwar kasuwa.
Sunusi Haruna daya ne daga cikin masu filaye a unguwar ya ce sun sayi filayen domin ginawa kuma suna da takardu amma rana tsaka ana shirin kwace musu.
Gwamnan Kano ya umarci sarakunan jihar su ci gaba da gudanar da bikin hawan sallah
Tarihi: Malamin da ya fara tafsiri a Najeria
Ya ce basu da karfi wasu ma da kyar suka tara kudin, wasu da ba shi suka mallaki gurin amma a yanzu ana so a kwace musu.
Ya ce sun ji sanarwa ne ta ka kuma a iya zaton su gwamna be san za a kwace musu filaye ba.
Alhaji Gambo Saminu sa ya ce sun ji kishin-kishin cewa za’a dawo da kasuwar ‘Yan Lemo da ta ‘Yankaba.
Ya ce akwai ishasshen fili a kasuwar Dangoro da za a mayar da kasuwannin ba tare da an kwace musu filaye ba.
Ya ce gurin ba gonaki bane mallakinsu da suka saya da gumin su a don haka suke neman daukin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.
Ya ce akalla sun kai mutum dubu 2 da suka mallaki filaye.
”Yawancin mu kananan ma’aikata ne da ‘yan kasuwa da muka mallaki wannan fili amma ana tagayyara mu,” a cewarsa.
Ya ce akwai kanannan ma’aikata na kwalejin Sa’adatu Rimi da suka sayi guraren ta hanyar tara kudi.
Nuraini Adebayo, ya nemi da a kawo musu dauki, yana mai cewa kwace musu filaye zai tagayyara rayuwar da dama daga cikin su.
Ko da muka tuntubi ma’aikatar kasa ta jihar Kano kan wannan korafi daraktan wayar da kai na ma’aikatar Murtala Shehu Umar ya ce ba shi da masaniya kan zargin kwace filayen.
Sai dai ya ce zai bincika zargin mutanen tare da tuntubar mu da wuri.
