
Hukumar Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce iyalan da ke maƙalle a birnin El Fasher da ke Sudan sama da shekara guda na cikin tsananin Yunwa.
Shirin ya kuma yi gargaɗin cewa babu alamar kawo ƙarshen mamayar dakarun RSF.Mayaƙan RSF na ta kokarin ganin sun ƙwace illahirin birnin da ke arewacin Darfur daga Sojojin Sudan da ke iko da birnin.
Tun cikin watan Afrilu ne mayaƙan na RSF suka yiwa birnin Kawanya, tare da datse hanyoyin kai abinci da sauran kayan tallafi ga dubban mutanen da ke maƙale ke buƙata.
Kwamitin shirin ya ce iyalai da dama sun koma cin abincin dabobbi da abinci da ya lalace domin su rayu.